Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hasashen Kaiwa Da Komowar Zaratan Kwallo A Kaka Mai Zuwa


Kungiyar Juventus

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus zata mai da hankalinta wajan zawarcin dan wasan tsakiya na Paris-saint German, mai suna Adrien Rabiot, dan shekaru 23 da haihuwa, in har dan wasan Arsenal Aaron Ramsey, mai shekaru 27 yaki amincewa da komawa kulob din na kasar Italiya.

Akwai labarin cewar matashin dan wasan tsakiya dan kasar Spain mai taka Leda a kungiyar Manchester City, mai suna Brahim Diaz, mai shekaru 19, a duniya zai koma kulob din Real Madrid a watan Janairu da zaran an bude hada hadar 'yan wasa.

Tsohon Darektan wasanni na kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Massimiliano, yace kulob din tayi yunkurin sayen dan wasan Juventus, dan kasar Putugal Cristiano Ronaldo, a shekarar da ta gabata daga Real Madrid, aman tsohon Darektan Massimiliano Mirabelli, shi yaki amince wa da kasuwancin.

Har ila yau AC Milan ta fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kan sayen dan wasan tsakiyarta Cesc Fabregas, mai shekaru 31 da haihuwa.

Arsenal da Tottenham suke kan gaba wajan zawarcin dan wasan tsakiya na kungiyar Hoffenheim mai suna Nadiem Amiri, dan shekaru 22 a duniya wanda bai buga wasa ko daya ba a wannan kakar wasan sakamakon jinya da yake fama dashi.

Manchester United tace zata sanya dan wasan bayanta Eric Bailly, mai shekaru 24 a kasuwa a watan Janairu da zaran an bude hada hadar saye da sayarwa na 'yan wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG