Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar 'Yan Matan Najeriya Zasu Kara A Gobe Talata


Tawagar Kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya Super Falcons, gobe Talata, za su fafata a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin mata na Nahiyar Afirka wanda yake gudana a ka kasar Ghana.

Najeriya zata kara da takwarorinsu na Kamaru, sai kuma Banyana Banyana na Afrika ta Kudu za su fafata suma a wasan.

Super Falcons, ta lallasa takwararta ta kasar Equatorial Guinea da kwallaye 6-0, a wasan karshe na rukuni, wannan nasarar ita ta baiwa Najeriya damar kaiwa zagayen kusa da na karshe a gasar.

Bayan kammala wasan rukunin B da take ciki a matsayin na biyu da maki shida, inda ita kuma Afrika ta Kudu ke kan gaba da maki 7, bayan tashi wasa kunnen doki 1-1 tsakaninta da Zambia.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG