Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hasashen Yadda Kasuwar Saye-da-Sayarwar Zakaru A Bana Zata Kasance


Dan wasan gaba na kasar Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 21, ya neme ya bar Kungiyar Barcelona a lokacin da aka bude saye da sayarwan 'yan kwallon kafa a watan Janairu wanda hakan ka iya bai wa tsohon dan wasanta Neymar damar komawa Nou Camp daga Paris St-Germain bayan ta sai dashi.

Kungiyar kwallon kafa zasu kara da takwarar ta Juventus wajan zawarcin dan wasa mai tsaron raga na Manchester United David DE Gea mai shekaru 28 da haihuwa dan kasar Spain.

Manaja Everton Marco Silva yace nayi shirin gwada karfi wajen nuna son dan wasan Barcelona, da ke yi wa dan wasa mai shekara 25 da haihuwa Andre Gomes, wanda yake Goodison Park a matsayin aro, domin ya koma a mazaunin dindindin.

Dan wasan Chelsea Eden Hazard, dan shekara 27,da haihuwa ya fasa komawa Kungiyar kwallon kafa Paris St-Germain, kamar yadda ta bukata, sai dai ya bayyana ra'ayinsa na cewar zai iya barin Stamford Bridge a cikin bazara.

Daraktan Kungiyar AC Milan Leonardo, na tattaunawa da kulob Chelsea kan batun dan wasan tsakiya Cesc Fabregas, mai shekara 31, da 'yan wasan
baya Gary Cahill, mai shekara 32, da kuma Andreas Christensen, dan shekara 22, da haihuwa.

Dan wasan Barcelona' Jordi Alba, dan shekara 29, a duniya ya ce kulob din bai sabunta kwantarakinsa ba, don haka babu tabbas a kan makomarsa a Kungiyar.

Manchester United tana da ra'ayin sayen dan wasan Roma na kasar Itali dan shekara 22 a duniya mai suna Lorenzo Pellegrini, bayan da kulob din ta fahimci cewa zata iya yin amfani da wata dama wajan sayen sa a karshen
kakar wasa ta bana.

Rafa Benitez manajan kulob din Newcastle ya ce bai fitar da ran sake komawa gasar Serie A na Itali ba nan gaba amman idan ya gaza cimma burinsa a St James' Park.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta jera sahu guda wajan zawarcin matashin danwasan gaba na Liverpool Bobby Duncan, mai shekaru 17 da haihuwa, dan uwa ga tsohon danwasan Liverpool din Steven Gerrard.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG