Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Duniya Sun Shiga Riga Daya


Kungiyoyin Liverpool, Barcelona, da Bayern Munich sun jera sahu daya, wajan zawarcin dan wasan Frankfurt mai shekaru 22 Luka Jovic, wanda a yanzu shine danwasan da yafi zurara kwallaye a gasar Bundusliga na kasar Jamus.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp, ya musanta rade radin da akeyi na cewar dan wasan tsakiyar kulob din Fabinho, dan shekaru 25, a duniya zai bar Kungiyar.

Danwasan tsakiya na Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, dan kasar Faransa Paul Pgoba, mai shekaru 25 da haihuwa ya nuna sha'awarsa, na barin kulob din domin komawa tsohowar Kungiyarsa ta Juventus, Kungiyar ta bukaci Manchester United, sanin matsayin danwasan a kulob din a wata tataunawa da suka fitar a Turai.

Arsenal tana zawarcin dan wasan tsakiya na Villarreal mai suna Pablo Fornals, dan shekaru 22, da haihuwa a shirye shiryen ta na sayen 'yanwasa a watan Janairu da zaran an bude hada hadar 'yanwasa.

Itama kungiyar AC Milan ta bayyana aniyarta na ganin ta dauko dan wasa mai tsaron baya na Chelsea Gary Cahill, mai shekaru 33 da haihuwa a watan Janairu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG