Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Haramtama Kungiyar Chelsea Siyan Zaratan 'Yan-Wasa


Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila tana fuskantar hukunci na dakatar da ita daga sayen sabbin 'yan wasa, bayan bincike da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta gudanar akanta.

An zargi kungiyar ta Chelsea ne da sayen wasu 'yan wasa wadanda ba su cika shekara 18 a duniya ba.

Inda aka samu wasu bayanai daga shafin yanar gizo na (Football Leaks) inda suka bayyana cewar ana binciken kungiyar tun shekara uku sakamakon sayen wasu 'yan wasa 19 wanda suka hada da Bertrand Traore.

'Yan wasa 14 daga cikin 19 ba su cika shekara 18 da haihuwaba, sai dai wata sanarwa da kungiyar ta Chelsea ta fitar, ta ce ta bai wa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA cikakken hadin kai bisa wannan lamarin.

Chelsea ta ce "ta gabatar da wasu hujjoji inda ta nuna yadda ta bi ka'idojin hukumar FIFA.

Shafin ya bayyana cewar bangaren ladaftarwa na hukumar FIFA ya umarci da a haramta wa Chelsea sayen 'yan wasa har na tsawon shekara biyu da kuma cin ta tarartar kudin Ingila da ya kai fam dubu 45.

A shekarar 2017 cikin watan Satumba aka fara binciken kungiyar kan wannan batu da ya ke neman haramta mata sayen 'yan wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG