Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Super Eagle Zasu Kara Da Kungiyar Bafana Bafana


Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles dake tarayyan Najeriya, su 22 ne yanzu haka suke karban horo a filin wasa na tunawa da Stephen Keshi dake Asaba na jihar Delta, karkashin jagorancin kocin kungiya Gernort Rohr, domin tunkarar wasan neman cancatar shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika, wanda zasu kara da takwarorinsu na Bafana Bafana dake kasar Afrika ta kudu a birnin Johannesburg, ranar Asabar mai zuwa.

Tawagar ta Super Eagles ta kunshi jagoran Kungiyar wato Ahmed Musa, sai kuma masu tsaron raga Daniel Akpeyi, Theophilus Afelokhai Ikechukwu Ezenwa.

A bangaren masu tsaron baya akwai Olaoluwa Aina, Adeleye Aniyikaye, Semi Ajayi, Bryan Idowu, William Ekong, Leon Balogun, Kenneth Omeruo
da kuma Jamilu Collins.

Sauran sun hada da 'yanwasan tsakiya wadda suka hada da Oghenekaro Etebo, John Ogu, sai Mikel Agu, A jerin 'yan wasa masu zura kwallo a raga kuwa, a kwai Kelechi Iheanacho, Moses Simon, Victor Osimhen, Henry Onyekuru, Alex Iwobi, Isaac Success da kuma Samuel Chukwueze.

Inda ake tsamanin isowar Samuel Kalu a yau dinnan, Bafana Bafana dai ta lallasa Super Eagles da ci 2-0 a Uyo jihar Akwa Ibom, a karawarsu ta farko.

Ana sa ran cewar tawagar ta Super Eagles zasu bar Najeriya zuwa kasar Afirka ta kudu a gobe Alhamis, domin isa kasar ta Afrika ta kudu kafin ranar Asabar da zasu kara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG