Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Ayau Za'a Cigaba Da Fafatawa A Gasar Cin Kofin Turai


A yau alhamis za'a dawo cigaba da fafatawa a wasannin kwallon kafa na cin kofin Turai (Europa League) 2018/19 a matakin rukuni.

Inda kungiyoyin kwallon kafa guda 48, da suka fito daga kasashen Turai zasu kece raini a wasannin 24.

Wasan farko za'ayi shine da misalin karfe hudu da minti hamsin na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da kasar Chadi, tsakanin Fanerbach na kasar Turkiya da Anderlecht dake Belgium, sai kuma Astana da Jablonec.

Da misalin karfe shida da minti hamsin da biyar kuwa za'a buga wasannin ne kamar haka, Akhisarspor da Sevilla, FK Krasnodar da Standard Liege, FC Astana zasu kece raini da FK Jablonec, Dynamo Kiev, da Rennes.

BATE Borisov kuwa zata karbi bakuncin Chelsea sai MOL Vidi da PAOK Salonika, Lazio da Olympicos Marseilles, Spartak Moscow, da Rangers, Gent da Basekktas, Apollon Limassol, da Frankfurt na kasar Jamus, Malmo na kasar Sweden da Sparsborg.

Sai kuma wasan karfe tara na yammaci Celtic su kara da RB Leipzig na kasar jamus, Real Betis da AC Milan, Arsenal a kasar Ingila zasu karbi bakuncin Sporting dake kasar Portugal, sai Girondis da Zenit, Bayern Leverkusen da Zurich, Vorskla Poltava da FK Qarabag.

Sauran wasannin kuwa sun hada da Dinamo Zagreb da Spartak Trnava, sai Olympiakos da F91 Dudelange, Slavia Prague FC da Copenhagen.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG