Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasa Joe Cole Yayi Murabus Daga Taka Leda


Tsohon dan wasan kwallon kafa na tsakiya a kasar Ingila da kuma Kungiyar Chelsea mai suna Joe Cole ya bayyana ajiye takalman buga wasansa, yana da shekaru 37 da haihuwa.

Dan wasan Cole, ya soma buga wasansa ne daga rukunin matasa na WestHam, daga bisani ya komo kulob din Liverpool, da Lille, Aston Villa da kuma Coventry City, har ila yau ya fafata wasa a kulob din Tampa Bay Rowdies.

Ya samu nasarar zurara kwallaye 10 cikin wasanni 56 da ya buga wa kasar Ingila tun daga shekara ta 2001 zuwa 2010. Dan wasan yace ya dade yana mafarkin hakan.

Bayan haka yace yana fatan nan da shekara 20 masu zuwa zaiyi waiwaye mai amfani kan shekaru 20 da suka gabata game da rayuwasa na kwallon kafa da yayi.

Tun yanada shekaru 17 da haihuwa, ya soma buga wasa a Kungiyar matasa na WestHam, sannan ya zama kaftin dinta na tsawon shekara hudu.

A shekarar 2003, ya koma Chelsea, inda ya samu nasarar daukan kofin gasar Firimiya, har sau uku da kofin kalu bale na FA sau biyu sannan
ya kai zagayen wasan karshe na gasar Zakarun Turai a shekara ta 2007 zuwa 2008.

Ya shafe shekaru takwas tare da tawagar Kungiyar Chelsea a Stamford Bridge, Inda ya buga wasanni sama da 280, a dukkannin wasannin ta. Cole ya kara da cewar, abu na musamman a rayuwarsa shi ne lashe kofin da ya yi a Chelsea, wani abune wanda ba zai taba mantawa a rayuwarsa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG