Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasa Kevin De Bruyne Zai Koma Fagen Taka Leda


Dan wasan tsakiya na Manchester City Kevin De Bruyne na shirin dawowa filin wasa, bayan raunin da ya samu a gwiwarsa a wasansu da sukayi tsakanisu da Fulham a gasar Qaraboa Cup, na kasar Ingila ranar 1 ga watan Nuwamba da muke ciki.

A baya an bayyana cewar danwasan zai shafe sati shida inda zai dawo wasa ranar 2 ga Disamba a wasan da za suyi da kingiyar Watford. Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid na shirin nada Santiago Solari a matsyain sabon manajanta wanda zai ja ragamar Kungiyar zuwa karshen kakan wasa na gaba.

Solari dai a yanzu yana rikon kwarya ne a kulob din bayan da ta sallami kocinta Lopetegui. Tsohon kocin Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Antonio Conte, yace ba zai amshi wani tayi na zamowa mai horas da 'yanwasa ba, har sai ya tsaya ya ga yadda karshen kakan wasan bana zata kare.

Sakamakon yana jiran tsohowar kulob dinsa Chelsea ta biyashi wasu kudi da suka kai fam miliyan 11 bayan da ta sallame shi, yana da sauran kwantirakin shekara guda da Kungiyar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG