Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Yace Kungiyarsa Ba Tayi Rawar Bakin Hantsiba


Dan wasan Juventus-Ronaldo

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus Cristiano Ronaldo ya ce tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United sam ba ta cancanci samun nasara a wasan da ya gudana tsakaninta da Juventus ba, a ranar laraba da ta gabata na zakarun turai.

Wasan dai Manchester United ta samu nasara akan Juventus da ci 2 da 1 a na daf da tashi.

A cewar dan wasan Cristiano Ronaldo, wanda shi ya zura kwallo daya da Juventus ta sha a wasan cikin minti na 55 da fara wasa, Juventus ta yi rawar gani a wasan kuma babu shakka, da ita ya kamata ta samu cikakken dama da ya kamata ta ragargaza Manchester United.

Wannan shine karon farko da kulob din Juventus ta sha kaye cikin wasanni 15 da tabuga tun bayan dawowar Ronaldon Kungiyar a farkon kakan wasan bana daga Real Madrid a watan Yulin da ya gabata.

Bayan haka ita ke saman teburin gasar Series A, na kasar Itali a bana. Kuma ita take kan gaba a rukunin (H) na cin kofin zakarun turai da maki 6 sai Manchester United take biye da ita da maki 7.

Ronaldo yace dole ne ‘yan wasan Juventus su zage damtse, la’akari da
muhimmancin gasar matukar dai suna son a daga kofin na zakarun Turai a wannan shekara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG