Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasa Rafael Van der Vaart Yayi Murabus Daga Taka Leda


Tsohon dan wasan kwallon kafa na Kungiyar Tottenham da Real Madrid Rafael Van der Vaart mai shekaru 35 da haihuwa, ya ajiye takalman wasansa na din din din.

Dan wasan wanda tsohon mai buga wa tawagar Kungiyar kwallo kafa na kasar Netherland ne wanda ya taimaka mata a gasar cin kofin Duniya na shekarar 2010, inda ta kai wasan karshe tsakanin ta da kasar Spain.

Ya shafe shekaru 18 yana taka leda tun daga Kungiyar kwallon kafa ta Ajax dake Nertherland ya buga wasanni 117, wa Kungiyar ta Ajax ya samu nasarar lashe lig din kasar sau biyu kafin ya koma kulob din Hamburg a shekara ta 2005.

Daga bisani ya canja sheka zuwa Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kasar Spain a shekaru ta 2008, kafin ya koma zuwa kulob din Tottenham na kasar Ingila bayan shekaru biyu ya fafata wasannin har 67, ya samu nasarar jefa kwallaye 24 a lokacin.

A shekara ta 2012 ya sake komawa tsohowar kulob din sa na Hamburg, daganan ya shiga kulob din Danish Esbjerg a watan Agusta, amma saboda
rauni da yake fama dashi, wasanni uku kacal ya buga mata.

Inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunci yace abu mai sauki a gareshi yanzu, shine ya ajiye takalman wasansa duk da kasancewar ya na da sha'awar yin ta.

Ya kara da cewar kalmomisa ba za su cikaba sai yayi gode wadannan shekaru 18 da yayi cikin wannan sana'a ta kwallon kafa da kuma godiya ga dinbin magoya bayansa a lokacin yana taka leda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG