Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Real Madrid Ta Sallami Kocinta Julen Lopetegui


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bada sanarwar Sallaman kocinyanta Julen Lopetegui, mai shekaru 52, da haihuwa bayan watanni hudu da rabi da yayi da kama aiki a Bernabeu, a matsayin mai horaswa.

Lopetegui, ya karbi aikinne a wajen tsohon kocin Real Madrid, Zinadine Zidane wanda ya ajiye aikinsa rana tsaka a Kungiyar.

Kocin Lopetegui ya gaza samun nasara a wasanni daban daban har guda biyar a jere da ya jagoranta da tawagar Kungiyar ta Real Madrid inda a ranar lahadin da ta gabata kulob din ya sha kashi a babban wasan da ya buga da Kungiyar Barcelona, inda aka lallasa Real da ci 5 da 1.

Real Madrid dai ta kasance a matsayi na tara a teburin laliga mako na 10 a bana, wadda rabonta da ta tsinci kanta a wannan yanayin tun shekarar 2001 zuwa 2002.

Lopetegui, ya jagoranci tawagar Kungiyar wajan motsa jiki a ranar litinin din nan da safe kafin nan hukumar kulob din tayi zama ta yanke hukumcin sallamarsa.

Wannan shine karo na biyu da ake Sallamar Lopetegui, a matsayin mai horaswa cikin shekara guda domin kasar Spain ta sallameshi a saura kwana biyu a fara gasar cin kofin duniya na 2018, bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar Spain ta samu labarin ya kulla yarjeniya da Real Madrid.

Tuni dai Kungiyar ta bayyana sunan tsohon dan wasanta wanda yake rike da karamar Kungiyar Real Madrid mai suna Santiago Solari, a matsayin wanda ya maye gurbin Lopetegui.

Real Madrid tace akwai babbar matsala tsakanin ingancin ma'aikatarta da irin Sakamakon da Kungiyar take samu.

Sabon kocin Santiago Solari, zai fara jagorantar kulob din a wasan da zata yi ranar laraba tsakaninta da Kungiyar Segunda, a gasar Spanish Cup.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG