Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Kocin Chelsea Antonio Conte Yaki Yarda Da Sulhu


Koci Antonio Conte

Tsohon kocin kungiya kwallon kafa ta Chelsea Antonio Conte, ya ki ya sadu da jagororin Kungiyar Chelsea inda ya dage kan daukar su zuwa kotu game da sauran albashinsa.

Conte, yana bukatar Kungiyar ta Chelsea da ta biyashi sauran albashinsa, wanda ya kai fam miliyan 8.7 domin ta rabu dashi ba bisa kan ka'idaba.

Kungiyar ta Chelsea dai ta sallami Kocin ne daga aikin sa bayan yana da sauran shekara guda kan yarjeniyar da sukayi.

Sai dai Kungiyar ta Chelsea tace taki biyansane saboda wasu halaiyarsa a kulob din, ciki har da ya kasa lura da Diego Costa a Kungiyar.

Chelsea dai tayi kukarinta na bukatar da suyi ganawar ido da ido, tsakaninta da tsohon kocinta Antonio Conte, kan wannan lamarin ba sai a cikin kotu ba, amman Conte yaki amincewa da batun zaman da aka nemeshi dan sasantawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG