Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohuwar Kungiyar Danwasa Wayne Rooney Zata Karrama Shi


Mai horar da tawagar 'yan kwallon kafa na kasar Ingila Gareth Souhgate, ya ce ya kamata ‘yan wasan kasar Ingila su san tarihin gudunmawar da tsohon dan wasan gaba na kasar Wayne Rooney ya baiwa kasar, a lokacin da yake taka mata leda domin su rika mutuntashi.

Gareth Southgate ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani kan wasu kalamai da wasu sukeyi, na sukarshi kan matakinsa na gayyatar Rooney domin bugawa tawagar Ingila wasan sada zumunci, da za suyi da kasar Amurka a mako mai zuwa, ranar Alhamis mai zuwa 15 ga watan Nuwamba 2018.

Kocin ya kara da cewar an shirya wasan ne musamman domin karrama dan wasan, inda aka masa lakani da taken “Rooney Foundation International”

Sai dai a ranar wannan wasan tsohon danwasan Rooney zai shiga fili ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, haka zalika ba zai sanya kambun kaftin ba, ba kuma zai sanya riga mai lamba 10 da ya saba sanyawa a lokacin da yake cikin tawagar Ingila ba.

Danwasan Rooney mai shekaru 33, da haihuwa ya bugawa kasarsa ta Ingila wasanni har guda 119 inda ya samu nasarar zurara kwallaye guda 53, wasa na karshe da ya bugawa Ingila shi ne wanda suka fafata da kasar Scotland a
watan Nuwamba na shekarar 2016.

Daga nan kuma ya ajiye takalman wasansa wa kasar inda ya mai da hankali kan wasan da ya keyi a kulob din sa, wanda yanzu haka yake tawagar Kungiyar kwallon kafa ta DC United dake kasar Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG