Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasa Eden Hazard Baya Shirin Kauracema Kungiyarsa


Thorgan Hazard, dan uwa ga dan wasan Chelsea Eden Hazard yace dan uwasan ba zai bar Stamford Bridge zuwa Kungiyar Real Madrid kamar yadda take da muradin sayen danwasan mai shekaru 27 da haihuwa.

Shi kuwa dan wasan gefe na Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane, mai shekaru 26, a duniya yayi watsi da batun matsayin kwantirakinsa a Kungiyar, inda yace shi yanzu haka yana jin dadin zama a Kungiyar tasa.

Har ila yau Chelsea da Manchester City sun jera sahu guda wajan zawarcin matashin danwasan Kungiyar Sunderland mai suna Bali Mumba, mai shekaru 17 da haihuwa, wanda ya buga wasanni hudu kacal wa kungiyarsa a kakan wasan bana.

Dan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey na iya komawa Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, bayan da kulob din mai buga gasar Bundusliga ta nuna sha'awarta kan danwasan yayin da kwantirakinsa yake shirin karewa a Kungiyar Arsenal.

Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea Andy Townsend da kuma tsohon dan wasan Manchester United Owen Hargreaves sun bayyana cewa danwasan tsakiya na Najeriya Philip Billing na iya barin kulob din sa na Huddersfield Town in har Kungiyar ta tafi Relegation a karshen kakan wasan bana

Dan wasan dai ya haskaka a wasan da suka doke Fulham daci 1-0 a ranar litinin da ta gabata a gasar firimiya lig na kasar Ingila.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG