Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Fadan Da Ya Kacame An Dakatar Da Wasu 'Yan Wasa


Tsohon dan wasan Kungiyar kwallon kafa na Tottenham Roberto Soldado, ya kasance daya daga cikin 'yan wasa biyar da aka dakatar a wasan da aka fafata tsakanin Galatasaray da Fenerbahce.

Sakamakon wata hatsaniya da ta kaure tsakanin mambobin kulob din biyu inda sukayi ta ba hammata iska a wasan da aka tashi 2-2.

Soldado, mai shekaru 33, da haihuwa wanda ya shiga Fenerbahce daga Villarreal a shekara ta 2017, yana daya daga cikin 'yan wasa uku, kuma an dakatar dashi na tsawon wasanni shida.

Shi kuwa dan wasan Fenerbahce Jailson Siqueira, an dakatar dashi a wasanni takwas sai Badou Ndiaye na Kungiyar Galatasaray wanda aka dakatar dashi na wasanni biyar.

Shi kuwa jagoran Kungiyar Galatasaray mai suna Faith Terim, an haramtamasa tsayuwa akan layi na wasanni 7 sakamakon cin mutumcin alkalin wasa da yayi, haka kuma mataimakin sa Hasan Sas dukkansu na wasanni 8.

Dan wasan tsakiya na Galatasaray Garry Mendes Rodrigues, da takwaransa Ryan Donk an dakatar dasu wasanni uku ne da kuma wasanni shida.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG