Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Da Lionel Messi Zune Zakarun Duniyar Kwallo


Kylian Mbappe, ya ce indai a bangaren tamolace, to har yanzu babu kamar Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

Sai dai ya kamata su san da cewar bajintar da ya nuna a lokacin gasar cin
kofin duniya na bana da akayi a Rasha, na iya bashi damar lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya ta Ballon d’Or.

Matashin dan wasan Mbappe mai shekaru 19 da haihuwa ya bada gaggarumar gudunmawa ga kasar sa Faransa wajen samun nasarar lashe kofin duniya.

Domin shi ya zura mata kwallaye har guda 4, hakan ya bashi damar samun
kyautar gwarzon matashin dan wasa a gasar da yafi duk wani matashi kokari a bana.

Kuma ya kafa tarihin matashi na biyu mafi karancin shekaru da ya ci kwallaye
a babbar gasar kwallon kafa ta duniya, tun bayan Pele da ya soma kafa Tarihin a shekarar 1958 a lokacin da yake da shekaru 17 a duniya.

A bangaren Ligue 1 na kasar Faransa kuwa Mbappe ya kasance danwasan da yafi yawan kwallaye a shekarar da ta gaba ta, a karkashin kungiyarsa ta Paris Saint Germain inda yaci kwallaye har guda 11.

A har yanzu babu wani dan wasan kwallon kafa da ya kai Cristiano Ronaldo da Lionel Messi yawan lashe kyautar gwarzon dan kwallon na duniya ta Ballon d’Or, inda kowannen su ya karbi wannan kambun sau biyar, sun shafe shekaru 10 suna kaka gida wajan lashe wannan a tsakanin su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG