Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Real Madrid Zata Sayo 'Yan-Wasa A Watan Jainairu


Kungiyar Real Madrid tace ya zamo dole ta saye danwasan gaba a watan janairu, da zaran an bude hada hadarwar saye da sayarwa na 'yan wasa, sakamakon ta fara cire tsammani abunda take bukata daga 'yan wasanta Gareth Bale da Benzema.

Itama Barcelona tace tana bukatar sayen dan wasa mai tsaron baya, a watan janairu bisa la'akari da raunin danwasanta Samuel Umtiti mai shekaru 25 da haihuwa da yake fama dashi.

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan dake kasar Itali ta fara tataunawa kan sayen danwasan tsakiya dan kasar Spain mai taka leda a kulob na Chelsea, mai suna Cesc Fabregas, dan shekaru 31, da haihuwa.

Manchester United tana shirye shiryen ninka albashin dan wasan tsakiya na Kungiyar Roma, dake kasar Itali mai suna Lorenzo Pellegrini, dan shekaru 22 a duniya, inda ake alakanta cewar United zata biya fam miliyan 26 domin sayen danwasan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG