Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayern, Manchester United Na Zawarcin Zidane


Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus, ta maida hankalinta wajen daukan Zinedine Zidane a matsayin sabon kocinta a cewar rahotanni.

Bayern na sa ran Zidane zai maye gurbin Niko Kovac.

Baya ga kungiyar ta Bayern, Manchester United ta Ingila ma na zarwarcin tsohon kocin na Real Madrid.

Koci Jose Maurinho na fuskantar barazanar sallama idan har bai kai kungiyar ga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ba a kakar wasa ta gaba.

Sai dai rahotanni na nuni da cewa, kungiyar ta Bayern na gaba da United wajen kokarin mallake Zidane.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG