Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Scott Parker Zai Zama Mataimaki A Kungiyar Fulham


Tsohon dan wasan tsakiya na kasar Ingila Scott Parker, mai shekaru 38, da haihuwa zai zama mataimakin Claudio Ranieri, a Kungiyar kwallon kafa ta Fulham.
Parker, wanda tsohon danwasan Kungiyar Fulham ne, ya shafe shekaru 3 ya na fafatawa da tawagar kulob din, inda ya buga mata wasanni 128.

Kafin zuwansa Fulham, Scott Parker, ya kasance jami'i a cikin kungiyar Craven Cottage, ya kuma shafe kakar wasa guda a kungiyar matasa ta Tottenham Hotspur, na 'yan kasa da shekaru 18 a matsayin jagoranta lokacin da ya ajiye takalman wasansa.

A na sa bangaren kocin kungiyar Claudio Ranieri, ya yaba bisa samun mataimaki mai kwazo wanda zai taimaka masa wajan gudanar da aiyuka a kungiyar ta Fulham, domin samun nasarori na cigaba.
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG