Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tabbacin Ficewar Dan Wasa Marcus Rashford Daga Kungiyarsa


Shugaban Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ed Woodward, yace Kulob din zai tatauna da dan wasan gaba nasu Marcus Rashford, mai shekaru 21 da haihuwa kan batun tsawaita zamansa a Kungiyar kafin zuwa karshen kakar wasa na bana.

Inda za'a biya danwasan fam dubu 150 duk sati domin ta haramta masa komawa Kungiyar Real Madrid da Paris Saints German wanda duk kan ninsu suke zawarcin danwasan.

A yanzu dai dan wasan Rashford, yana karban fam dubu 75 ne duk sati daga United, kwantirakinsa zata kare ne a shekara ta 2020 tare da zaɓi na wani karin watanni 12.

Har ila yau Manchester United, a halin yanzu, tana gwagwarmaya wajan ganin ta kulla yarjejeniya da dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Roma dake Itali mai suna Lorenzo Pellegrini.

Giampiero Pocetta, shine wakilin danwasan Lorenzo ya sha fadar cewar dan wasan mai shekaru 22, da haihuwa zai koma Manchester United a watan Janairu da zaran an bude hada hadar 'yanwasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG