Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Manchester Da Chelsea Sun Jera Sahu Wajen Sayan Dan Wasa


Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Spain, ta bukaci kawo karshen zaman tsohon dan wasanta dan kasar Brazil Neymar dan shekaru 26 da haihuwa a kulob dinsa na PSG, domin dawowa gareta bayan ta sai dashi wa Kungiyar akan kudi yuro miliyan 222.

Chelsea da Manchester United sun jera sahu guda wajan zawarcin dan wasan Inter Milan, dan kasar Slovakia mai suna Skriniar, dan shekaru 23 a duniya, wanda aka bashi darajar fam miliyan 75 a duk Kungiyar da take son sayan shi.

Dan wasan gefe na kungiyar Borussia Dortmund Christian Pulisic mai shekaru 20 da haihuwa wanda ake alakantashi da komawa Liverpool, ya yaba wa kocin Kungiyar Liverpool Jurgen Klopp bisa salon yadda take horaswa, yace duk wani dan wasa burinsa shine yayi wasa a karkashin sa.

Tsohon dan wasan Barcelona Xavi wanda yanzu yake taka ledarsa a Kungiyar kwallon kafa na Al Sadd a kasar Qatar, yace yayi imanin nan gaba kadan kocin Manchester City Pep Guadiola, zai mayarda Manchester City kungiya mafi kyau a Nahiyar Turai.

Manchester United ta duba yuwar sayen dan wasan baya na Florentine mai suna Nikola Milenkovic, dan shekaru 21 da haihuwa a watan Janairu da zaran an bude hada hadar saye da sayarwa na 'yan wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG