Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Watan Junairu Kungiyoyin Kwallon Kafa Zasu Sayi 'Yan Wasa


Dan wasan tsakiya na Leicester city dan kasar Spain Vicente Iborra, mai shekaru 30, da haihuwa na shirin komawa tsohowar kulob dinsa Sevilla, a watan Janairu mai zuwa, sai dai Darektan kungiyar Joaquin yace akwai rikici game da komawar dan wasan.

Mai tsaron raga na kungiyar Burnley Joe Hart, dan shekaru 31, a duniya yace har yanzu bai cire tsammani na komawa cikin tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila ba.

Bayern Munich tana shirye shiyen dauko matashin dan wasan kungiyar kwallon kafa na Chelsea, a watan Janairu mai suna Callum Hudson-Odia, mai shekaru 18 da haihuwa wanda ya fafata wa tawagar 'yan kasa da shekara 18, na kasar Ingila a wasan cin kofin Duniya na 'yan kasa da shekaru 18.

Ana alakanta Kungiyar Juventus da takwarrata Inter Milan kan zawarcin sayen dan wasan tsakiya na Tottenham Mousa Dembele, dan shekaru 31 da haihuwa wada kwantirakinsa zai kare a kulob din karshen kakar wasan bana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG