Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kulob Da Sukafi Kashe Kudi A Gasar Firimiya Lig


Kungiyoyin kwallon kafa guda shida wanda suka fi kashe kudi a gasar firimiya lig na kasar Ingila.

Duk da cewar kungiyar Manchester City ita ta lashe kofin gasar firimiya na shekarar da ta wuce 2017/18, tana bayan Manchester United wajen biyan albashi, 'yan wasan kulub din na Old Trafford na kashe fiye da fam miliyan shida da rabi a duk shekara ga tawagar 'yan wasanta na farko.

Manchester City ce ta ke biye mata a matsayi na biyu inda take kashe fam miliyan £5,993,000, wajan biyan albashin 'yan wasanta.

Chelsea ce ta uku da ta ke kashe fam miliyan £5,020,004, sai Liverpool ta hudu mai kashe fam miliyan £4,862,963.

Sauran biyun cikin jerin shida sune Arsenal wace ta ke matsayi na biyar da albashin fam miliyan £4,853,130 ga 'yan wasan farkonta a shekara, da kuma Tottenham mai kashe fam miliyan £3,515,778.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG