Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jita Jitan Arsenal Za Ta Ajiye Dan Wasan Ta Mesut Ozil!


Sakamakon kin sanya dan wasan tsakiya na Arsenal da mai horas da kungiyar Unai Emery yayi, ya samu yabo.

Tsohon dan wasan Arsenal Wright ya yabawa kocin kungiyar Unai Emery, saboda rashin fargaba ko jin nauyin ajiye duk wani kwararren dan wasan kungiyar, da himmarsa ko kwazonsa yayi kasa.

Wright, ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan matakin da kocin ya dauka na ajiye dan wasansa Mesut Ozil, a benci yayin wasan da sukayi ranar Lahadin nan da ta wuce.

Arsenal ta samu nasara kan Bournemouth da kwallaye 2 da 1, a gidan Bournemouth.

Danwasan Ozil, shine dan wasan da yafi kowane dan wasa karban albashi mai tsoka a Arsenal, inda yake karban fam dubu 350,000 a kowane sati.

Rahotanni na nuni da cewar matakin ajiye Ozil dai kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito, na da nasaba da gazawarsa wajen taimakawa ga kulob din yadda ya kamata a wasanni uku da suka buga a jere inda sukayi canjaras a dukkaninsu.

Arsenal dai ta buga wasanninta har guda goma sha bakwai ba tare da an doketaba, a wasannin da suka hada da firimiya lig na Ingila, da kuma kofin Nahiyar Turai (Europe League).

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG