Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Mata 'Yan Kwallon Kafar Najeriya, Tayi Nasara


Kungiyar kwallon kafar mata na tarayyan Najeriya Super Falcons ta yi nasarar kaiwa ga wasan karshe na gasar cin kofin Nahiyar Afrika 2018,
gasar wadda ke gudana a kasar Ghana.

Najeriya ta samu wannan nasarar ne bayan da ta doke takwararta ta Matan Kamaru da ci 4 da 2, a wasan daf dana karshe (Semi Final).

An kai ruwa rana a wasan inda aka shafe tsawon mintuna 120 ana fafatawa tsakanin kasashen biyu ba tare da an zura kwallo ba, hakan ya sanya aka tafi bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalty).

Inda Super Falcons ta yi nasarar jefa kwallayenta hudu ita kuma Kamaru ta jefa biyu.

Wannan nasarar ta Super Falcons wata dama ce, yanzu ita ke rike da kambun kofin Afrika har guda 8 kai tsaye ya bata damar samun gurbi a gasar cin kofin duniya, bangaren mata da kasar Faransa za ta karbi bakunci a bana.

A farkon wasan da Najeriya ta buga daga matakin rukunin Afrika ta
kudu ta samu nasara kanta da kwallo daya mai ban haushi amma daga bisani a sauran wasanninta Najeriya ta lallasa Zambia da kwallye 4-0, bayan haka tayi kaca kaca da kasar Equatorial Guinea da kwallaye 6-0.

A daya wasan da aka buga tsakanin Kasar Afrika ta Kudu da kasar Mali wasan daf da na karshe an doke Mali da ci 1- 0.

A ranar Asabar 1/12/2018 za'a kara a wasan karshe tsakanin tawagarta Mata ta Najeriya da ta Afrika ta Kudu, da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da kasar Chadi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG