Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Najeriya Ahmed Musa, Ya Shiga Kungiyar Kasa-da-Kasa Leicester!


Dan Wasan Nijeriya Ahmed Musa
Dan Wasan Nijeriya Ahmed Musa

Shugaban klob din 'yan wasan kwallon kafar “Leicester” Claudio Ranieri, ya bayyanar da dalilin shi na zakulo da daukar dan wasan kungiyar kwallon kafar Super Eagle, Ahmed Musa. Shugaban kungiyar Mr. Claudio, ya bayyanar da hakan ne a shafin zumunta na kungiyar klob din.

Yace yana cike da matukar farincike na daukko dan wasa Ahmed, da yayi ya sakashi cikin gwarzayen ‘yan wasan kungiyar tashi. Yana da yakinin cewar dan wasan zai taka muhimiyyar rawa wajen ganin nasarar kungiyar a wasan firimiya dake nan gaba kadan.

Idan dai ba’a manta ba, a kakar wasanni da ta gabata yayi kuka da yadda ‘yan wasan nashi su kayi sanyi, amma da wannan sabon zubin, yana da tabbacin Ahmed, zai karama kungiyar wata zuma a fage. Ya kara da cewar Ahmed, dai na daya daga cikin mutane hudu 4, da kungiyar ta dauka a kwanakinan da tunanin cewar yana daya daga cikin ‘yan wasa da suke da gudu.

“Yan wasan dai zasu fara wasan su na farko, da kungiyar Manchester United, na wasan zumunta, a ranar bakwai 7, ga watan Agusta na wannan shekarar. Haka suna sa ran cewar Ahmed zai ci kwllaye a wasan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG