Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada - hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Kwallon Kafa Na Duniya


Yayin da ya rage saura wata guda a dawo wasanni na league league na kasashe daban daban, hankalin masu horas da 'yan wasan kwallon kafa na kungiyoyi daban daban a duniya ya karkata ne wajan nemo hazikan 'yan wasa domin su samu lashe wasannin kasashen da suke.

Ta dalilin haka ne kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar spain ta kammala sayen danwasan lyo maisuna Samuel Umtiti

Sai kuma kungiyar kwallon kafa ta chelsea na neman dan’wasan Leicester City maisuna N'golo kante

Mai horas da yanwasan Man City Pep guardiola na zawarcin dan’wasa daga kasar Colombia maisuna Marlos Moreno

Yayinda sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Man united Jose Mourinho yake shirye shirye domin sayar da ‘yan wasansa har guda 4 ‘yan wasan sune kamar haka

  1. Juan mata
  2. Marcos rojo
  3. 3 Daley blind
  4. 4 Schweinsteiger

Shi kuwa dan’wasan Nigeria Ahmed Musa ya baiyana jindadin sa na zuwa kungiyar kwallon kafa ta Leicester City.

Ita kuwa kungiyar Westham United tace dan’wasanta maisuna Dimitri Payet bana sayarwa bane

XS
SM
MD
LG