Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudi Ya Yanke Masu Minista Bashi Da Masaniyar Suna Amurka


'Yan Wasan Najeriya
'Yan Wasan Najeriya

Ministan matasa da wasani na Najeriya. Barista Solomon Dalung, yace bashi da masaniya cewa ‘yan Flying Eagles watau ‘yan kwallon Najeriya, ‘yan kasa da shekaru 23, akan tafiyarsu zuwa kasar Amurka, ba.

‘Yan wasan da Samson Siasia, mai horar dasu a makon da ya gabata ne suka nufin wani sansani dake Atlanta, a kasar Amurka, inda sue samun horo kafin su wuce Brazil, domin halartar gasar Olympics na bana wanda zai gudana a birnin Rio de Janeiro, ta kasar Brazil.

Da yake amsa tabayoyin manema labarai akan dalilin rashin kaiwa ‘yan wasan dauki domin an kusa korar su daga Otal din da suke Ministan yace shi daga bakin manema labaran yake samun labarin a karon farko.

Ministan yakara da cewa basu fadamana abinda suka je yiba kuma wanene ya kai su, yana mai cewa domin suna ‘yan wasan Najeriya, sun je kasar Amurka, suna da matsala yaya wannan ya zama matsalar mu.

Dalung, yace wa manema labarai shin da suka tashi tafiya kasar Amurka, an ce maku sun sanarda mu, yakamata ku manema labarai ku kafin ku kalubalance mu ku yi bincike ko muna da masaniya ko kuma a’a.

XS
SM
MD
LG