Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Spain ta bada sanarwar janyewa daga cikin masu zawarcin dan wasan kasar Faransa mai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Juventus Paul Pogba mai shekaru 23 daga cikin masu zawarcin sa.

Ita dai kungiyar Real Madrid ta bada sanarwar hakanne a sakamakon tsadar da tace dan wasan yayi domin kungiyar Juventus tana neman kudi ne har sama da Fan miliyan dari ga duk mai bukatar dan wasan wanda zai zamo mafi tsada a cikin kakar wasannin bana.

Wata majiyar ta bayyana cewa kungiyar Manchester ta sa masa kudi fan miliyan dari domin ganin ta sayi dan wasan.

A Najeriya kuma ma’aikatar kula da wasanni da matasa ta bada sanarwar rasuwar jami’I mai kula da filin wasa na tunawa da sir Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi mai suna Malam Yakubu Dan shuwa, Talban nangere.

Daga karshe kungiyar kwallon kafa ta voa flamingo dake cikin garin Bauchi zata yi wasan goron sallah data saba yi duk shekara domin wayarwa da mata kai akan cutar cizon sauro ta maleriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG