Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata Mutane Su Yiwa Mawaka Kyakkyawar Fahimta


Nazir Bayero Abdulrahman
Nazir Bayero Abdulrahman

A yau dandali ya samu bakunci mawakin rauji, Nazir Bayero Abdulrahman wanda aka fi sani da Nazir el Boss, wanda ya shafe shekaru hudu a wannan sana'a.

Nazir, yace daya daga cikin kalubalen dake addabar mawaka shine har yanzu akwai wadanda basu san mahimmancin mawaka ba, kuma wasu na ganin mawaka tabkar masu gurbata tarbiya.

Ya kara da cewa amma mawaka su sun san abinda da suke yin yana mai cewa yakamata mutane su yi masu kyakkyawar fahimta akan harkokinsu na waka.

Ya ce burinsa ya zamo fitattacen mawakin da za’a sani a duniya mussamam ma a faggen waka da harshen Hausa.

A fannin tsegume kuwa mawaki na harshen turanci Iyanya na dab da fito da sabon album dinsa tare da bude sabon kamfaninsa na dab'I, kamar yadda manajan sa Obi Franklin ya bayyanawa manema labarai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

XS
SM
MD
LG