Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shafin Sada Zumunta Na Facebook Ya Dauki Matakan Inganta Tsaron Aika Sakonni


Ana sa ran kwanannan shafin sada zumunta na facebook zai dauki kwakkwaran mataki akan manhajarsa ta aika sako wato Messenger domin kare sakonnin masu amfani da ita daga masu satar bayanai ko leken asiri.

Yanzu haka Kamfanin na kan gwada sabuwar hanyar wadda yasa wa suna “sokonni cikin sirri” wadda keda tabbacin kare duk wani sako da mai amfani da manhajar ya aika.

Amfani da wannan fasaha na nufin daga wanda ya aika da sakon sai wanda aka aikawa kadai ne zasu iya bude sakon akan wayoyin su, bugu da kari ko ta facebook ma baza’a iya bude sakon ba sai dai ta messenger kadai.

Wannan fasaha ta sami karbuwa ‘yan kwanakin nan a yayin da hukumar tsaro ta FBI ta nemi kamfanin Apple ya bude wayar matashin nan da akai zargi sa da aikata ayyukan ta’addanci a kasar Amurka domin gaza bude bayanan sirrin da matashin yayi amfani dasu wajan kulle wayar.

Yanzu haka ma kamfanin facebook ya riga ya fara amfani da wannan fasaha a manhajar WhatsApp, kuma kamar yadda sanarwar ta bayyana, kwanannan manhajar facebook messenger zata bunkasa da wannan fasahar tsaro.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG