Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimiyya: Za'a Yi Amfani Da "Fara" Wajen Yakan Ta'addanci A Duniya!


Fara Don Yaki da Ta'addanci
Fara Don Yaki da Ta'addanci

Babu wata hallita da Allah, ya daura a doron kasa da bata da amfani daban-daban. Taron wasu masana kimiyyar tsirrai da hallitun dabbobi, a jami’ar Washington a nan kasar Amurka, sun fara gudanar da wani bincike, wanda suke ganin cewar za’a iya amfani da Fara, wajen wargaza shirye-shiryen ‘yan ta’adda a fadin duniya.

Farfesa Baranidharan Raman, jagoran binciken ya kara da cewar, sun kirkiri wata na’ura da za’a iya amfani da ita a kwakwalwar Fara, wanda ita fara tana jin kamshin abu fiye da kowane irin hallita, kuma zasu hada na’urar da kwakwalwar fara, sai a sake su suyi yawo, duk inda suka sauka idan akwai sinadaran hada boma-bomai idan suka shaki kamshin zai kai ga kwakwalwar su, wanda hakan zai nuna inda ‘yan ta’adda ke boyewa da hade-haden muggan makaman su.

Hukumar sojojin ruwa na kasar Amurka, sun ware zunzurutun kudade da suka kai kimanin dallar Amurka, dubu dari bakwai da hamsin $750,000, don gudanar da binciken. Mr. Raman, ya kara da cewar sun kirkiri hancin roba da zasu sakama duk fara da za’ayi amfani da su wajen gudanar da binciken. Suna sa ran da zarar faran suka shinshini wani mugun kanshi na wasu sinadaran kemikal to zasu sanar, inda suka hada kwakwalwar farar da wani talabijin mai nuna hoton abubuwa da ke gudana da rayuwar Faranin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG