Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Fati Nijar Sarautar Gimbiyar Mawaka


Mawakiya Fati Nijar
Mawakiya Fati Nijar

A ranar wannan Juma’ar da ta gabata Sarkin Borgu da ke jihar Neja a Najeriya, Barista Mohammad Sani Halliru Dantoro, ya nada fitacciyar zabiyar nan, Binta Labaran wadda aka fi sani da Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Borgu.

A yayin bikin nadin, Mai Martaba sarkin, ya bayyana cewa tun kafin mahaifinsa, Sanata Halliru Dantoro ya rasu ya yi alkwarin baiwa mawakiyar wannan sarauta, amma cikin ikon Allah sai ba'a yi bikin nadin ba har ya rasu. Don haka ne dan nasa ya cika alkawarin da mahaifinsa ya daukarwa mawakiyar.

A Jawabinta Fati Nijar, ta yiwa Allah godiya kuma ta godewa masarautar Borgu, da wanna karamawan da aka yi mata.

XS
SM
MD
LG