Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada - hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A bangaren saye da sayarwa tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya, kungiyar Juventus dake kasar Italy ta karawa dan wasanta Paul Pogba mai shekaru ashirin da uku da haihuwa kudin da take bashi duk sati.

Kungiyar kwallon tace zata biya dan wasan nata zunzurutun kudi fan dubu dari da talatin a kowane sati domin ya cigaba da zama a kungiyar, wannan sanarwa ta fito ne daga bakin manajan sa, sai dai har yanzu dan wasan bai fito yace komi ba.

Ita kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na zawarcin dan wasan kungiyar Westbrom akan kudi fan miliyan hamsin da daya da dubu dari biyu.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Everton na zawarcin dan wasan sporting Clube William Carvalho dan shekaru ashirin da hudu akan kudi fan miliyan ashirin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:16 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG