Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Dake Kan Gaba A Kwallon Kafa A Duniya


 Gianni Infantino
Gianni Infantino

Bayan kammala gasar Euro da na Copa America, na 2016, hukumar dake kula da wasan kwallon kafa na duniya (FIFA), ta fitar da jadawalin sunayen kasashe dake kan gaba ta fanin kwallon kafa a duniya.

Kungiyar kwallon kafa na kasar Argentina ita take kan gaba sai Belgium ke biyemata sai kuma Columbia ta ukku sannan Jamus ta hudu, ita kuwa kasar Chile itace ta zo ta biyar mai biyemata kasar Portugal a mataki na shida.

Sauran sun hada da kasar Faransa a matakin na bakwai yayin da kasar Spain ta zo matakin na takwas, Brazil tana mataki na tara ne inda kasar Italiya ta dare maki na goma sai Wales na matakin na goma sha daya.

Jadawalin ya ci gaba da kasar Uruguay a matakin na goma sha biyu, sai kasar Ingila, wace ta dawo kasa a mataki na goma sha ukku saboda rashin tabuka abin a zo a gani a gasar da aka kammala a nahiyar Turai.

XS
SM
MD
LG