Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabe Renato Sanchez A Matsayin Matashin Dan Wasa Na Bana


Renato Sanches
Renato Sanches

A yayin kammala gasar nahiyar kasashen Turai, kwamitin dake kula da yanayin ‘yan wasa na gasar cin kofin nahiyar kasashen Turai,wanda aka yi a kasar Faransa ta zaben dan wasan kasar Portugal Renato Sanchez,dan shekaru goma sha takwas a matsayin matashi dan wasa na bana, na gasar daya gudana a kasar Faransa.

Bayan kammala gasar nahiyar Turai, yanzu hankalin ya karkarta ne zuwa gasar Olympics wanda za’a gudanar a kasar Brazil, ranar 5, ga watan Agusta, kuma a kammala ranar 21, ga wannan shekarar 2016.

Ana sa ran kasashe 207, ne zasu halarci gasar inda zasu fafata a wasani daban daban har guda 28, a cikin wasanin har da kwallon kafa.

Kimanin mutane 10,500 ake sa ran zasu fafata a wasanin daban daban da za’a gudanar a gasar ta Olympic.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:30 0:00

XS
SM
MD
LG