Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Zai Tafi Jinyar Watanni Biyar


Shahararren dan wasan kwallon kafa mai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wasa Cristiano Ronaldo zai tafi jinyar watanni biyar a sakamakon raunin da ya samu a kafarsa ta hagu a wasan da suka buga da kasar Faransa a wasansu na karshe na cin kofin nahiyar kasashen Turai wanda aka gama ranar Litini a kasar Faransa.

Ronaldo ya fita daga wasan cikin minti na ashirin da biyar da fara wasan a sakamakon karon da suka yi da dan wasan kasar Faransa mai suna Dimitri Payet.

Ana sa ran cewa Cristiano Ronaldo zai dawo ya cigaba da taka leda a watan nuwambar shekar 2016, da muke ciki

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG