Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Zabi Cristiano Ronaldo A Matsayin (Fifa player of the year)


Hukumar dake kula da sha'anin wasan kwallon kafa ta duniya (Fifa) ta zabi Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal mai taka leda a yanzu haka a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, a matsayin dan wasan da yafi kuwa kwazo a bangaren tamola na wannan shekarar wato (Fifa player of the Year).

Ronaldo, ya doke abokin takararsa Lionel Messi, na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

A satin da ya wuce ne a ka zabi Cristiano, a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa ta duniya 2016, a karo na hudu wanda Kungiyar ‘yanjaridu na duniya sukayi zaben a kasan faransa

Har ila yau a ranar lahadi 18/12/2016 Ronaldo, ya jagoranci Kungiyarsa ta Real Madrid, wajan lashe kofin Fifa Club World Cup, 2016 inda suka samu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Kashima Antlers, na kasar Japan, daci 4 da 2, Cristiano ya samu damar jefa kwallaye 3 a cikin hudu da Real ta sha.

A yanzu haka Ronaldo, yana da kwallaye 55, a cikin wasanni 57, da ya buga wa kungiyarsa ta Real Madrid.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG