Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


 Sergio Ramos
Sergio Ramos

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, mai rike da kaftin na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Sergio Ramos ya nuna rashin jindadinsa na ganin yanda dan wasan Kungiyar James Rodriguez, ya matsa sai ya bar kungiyar ta Real Madrid.
kungiyoyi da dama ne Ki zawarcin dan wasan cikinsu harda Kungiyar Chelsea, wanda ta ware fam miliyan £75 domin sayensa.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta musanta rade radin da akeyi cewa Shahararren dan wasanta Lionel Messi, yaki ya sabonta kwantirakinsa a Kungiyar, mai horas da Kungiyar Luis Enrique, ya ce yana da tabbacin cewa dan wasan zai amince idan aka tuntubeshi a yanzu Barcelona, bata ma fara maganar ba.

Indan hakan ya tabbata ana sa ran cewa Lionel Messi, zai kasance yafi kowa daukar kudi a kungiyar ta Barcelona.

Calos Tavez na shirin zama dan wasan da zaifi kowa daukan kudi a fagen wasan kwallon kafa inda zai kasance yana karbar fam dubu £615,000 a duk sati daga kungiyar Shanghai Shenhua.

Kungiyar kwallon kafa ta Marseille ta koma neman tsohon dan wasanta Dimitri Payet, wanda yanzu haka yake taka leda a kungiyar Westham United dake Ingila

Juventus ta sake koma domin zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal mai suna Alexis Sanchez.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:26 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG