Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lionel Messi Zai Fi Kowane Dan Kwallo Albashi


Lionel Messi
Lionel Messi

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta sha alwashin maida Lionel Messi, dan kwallon da yafi kowa tsada a duniya, a wani yunkuri da kungiyar keyi na sabon tattaunawa da dan kwallon akan wani sabon kwanteragi a shekara mai kamawa,kungiyar a yanzu ta samuNeymar, Luis Saurez da Sergio, a hannu.

Gareth Bale da Cristiano, tuni suka rataba hannu wa abokiya hamayyar Barcelona, watau Real Madrid, inda a yanzu Ronaldo, shine dan wasan da yafi tsada inda yake karbar fam dubu 430,000,a ka=owane sati.

Shugaban kungiyar ta Barcelona, Josep Maria Bartomeu, yace kungiyar zata kashe duk abinda ya kama domin ta tabbatar cewa Messi, ya kasance a kungiyar.

Ya kara da cewa Messi, dan kwallon Barcelona ne kuma yana jida kungiyar a zuciyarsa, yace zasu zauna a New York, su tattauna dasji da wakilansa da kuma tabbacin cewa shi kansa Messi, ya san cewa yana kungiyar da ta cencenta ya kasance.

A batun kudi kuwa shugaban yace tunda shine da kwallon da yafi kowa a duniya ya kamata yafi kowa albashi.

XS
SM
MD
LG