Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mikel Zai Bar Kungiyar Chelsea


Daga dukkan alamu John Mikel Obi, na yunkurin barin kungiyar Chelsea, kamar yadda mai horar da ‘yan wasan Super Eagles, Gernot Rohr, ya ce Mikel, na zantawa da kungiyar kwallon kafa ta Olympique Marseille.

Ya Kara da cewa a lokacin da suka sadu a birni Ingila, tattaunawar ta kai wani mizani, koda yake Mikel, ya kwashe shekaru goma a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kwantareginsa zai kari a shekara maizuwa ne.

Mikel, mai shekaru ashirin da tara har yanzu bai bugawa Chelsea, daka wasa day aba a karkashin jagoranci Antonio Conte, tun bayan da Mikel, din ya dawo daga wasan Olympics inda ya jagoranci tawagar Najeriya, masu takawa kasar Leda.

Akwai rade raden cewa Manchester United da kuma wani kulub a kasar China na bukatarsa.

XS
SM
MD
LG