Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Ya Jefa Kwallonsa Ta Dari 500


A jiya alhamis kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasarar zuwa wasan karshe na cin kofin (Fifa Club WorldCup 2016)

Real ta samu nasaranne bayan ta doke takwararta ta Club America da ci 2 da 0, Real ta saka kwallonta na farko a ragar America cikin mintuna 45, da fara wasanta, kafin dan wasanta mai suna Benzema.

Daga bisani ana daf da tashi mintuna na casa'in daidai sai gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar ta America.
Sakamakon hakan ranar lahadi 18/12/2016, kungiyar ta Real zasu gwabza da kungiyar kwallon kafa mai suna Kashima Antlers, a wasan karshe

Shi kuwa Shahararre kuma gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo, ya jefa kwallonsa ta 500, a jiya yayin wasansu da America, a gasar Fifa club worldCup, a iya yawan wasannin da ya buga a yanzu haka Wanda ya kama daga kasarsa ta haihuwa Portugal, zuwa kulob kulob da ya bugawa wasanni.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG