Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Riyad Mahrez Ya Lashe Kyautar BBC Na Kwallon Afirka


Riyad Mahrez
Riyad Mahrez

Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Leicester City, da asalin kasar Algeria, Riyad Mahrez, ya lashe gasar dan wasan Afirka, da ya fi iya taka leda na gidan Radiyon BBC, na shekarar 2016.

Ya doke abokan takararsa ne kamar Pierre-Emerick Aubameyang, Andre Ayew, Sadio Mane da Yaya Toure, wanda ma’abota wasan kwallon kafa daga koina a duniya, ne suka jefa kuri’a domin zaben gwarzon dan wasan.

Da yake jawabi baya da aka mika mashi kyautar, Riyad Mahrez, yace yayi murna matuka yakuma godewa masoyansa da fatar zai ci gaba da taka leda yadda yakamat da yiwa kansa fatan alheri.

Mahrez, ya taka rawar ganin a nasarar da Leicester City, tayi na lashe gasar firimiya lig.

XS
SM
MD
LG