Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lionel Messi Zai Yi Aure


Shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Argentina, mai taka leda a kungiyar kwallon kafar Barcelona, Lionel Messi, zai yi aure a shekara mai zuwa.

Matar da ake sa ran cewa ita zai aura Antonella Roccuzzo, ta kasance buduwarsa tun yana mai shekaru goma sha ukku, kafin ya bar kasar Argentina, zuwa kasar Spain, domin taka leda.

Koda yake Lionel Messi, da Antonella, sun haifi ‘ya’ya biyu tare amma har yanzu basu yi aure ba kamar yadda aka gada.

Wani dan jarida, kuma na hannun daman Lionel Messi, watau, Juan Pablo, ne ya shedawa jama’a, hakan a shirin da yake gabatarwa a rediyo, a jiya laraba.

Pablo, ya kara da cewa koda yake ba’a bashi tabbacin ranar bas hi dai abinda ya sani shine cewa akwai gagarumin biki da za’a gudanar a Rosario, kuma ana gyayatar kowa.

XS
SM
MD
LG