Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Bai Cancanci Lashe Ballon D'or Ba


Tsohon dan wasan kwallon kafa na Barcelona, Xavi Hernandez, wanda yanzu yake taka leda a wata kungiya mai suna Al sad, dake can kasar Qatar, yace samsam dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo bai can canci abashi gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya (BALLON D'OR) 2016 ba.
A cewar Xavi babu abinda Cristiano Ronaldo, yayi sai dai cin kofuna guda biyu Kofin zakarun Turai wanda ya ci da kungiyarsa ta Real Madrid, sai kuma kofin nahiyar kasashen Turai na 2016 wanda kasar sa ta Portugal, ta lashe, bayan haka babu wani abinda dan wasan yayi.

Xavi yace indai ana batun iya kwallo ne in dai aka kawo Messi shikenan sai a rufe taro domin bashi da sa'an karawa a koina da kuma duk wani mutumin da yasan kwallon kafa yasan Messi yafi Cristiano dacewa.

Xavi ya ce bawa Ronaldo wannan kambin ba'ayi daidaiba in dan kawai bisa dalilanne

Sai dai Shima Cristiano Ronaldo ya maida martani bisa wannan kalamai da Xavi yayi akansa ya ce wannan abu da Xavi yake yi duk haushin rashine domin bai taba daukan Zakaran kwallon kafa na duniya ba Kuda sau daya ni kuwa na dauka sau ukku, wannan itace ta hudu.

Cristiano ya karbi wannan kambin na Ballon d'or a hannun Lionel Messi, wanda ya dauka sau biyar.

A na sa tsammanin Ronaldo zai fafata a wasan da kungiyarsa ta Real Madrid zatayi a gasar (Club World Cup) 2016 inda zasuyi wasan kusa da na karshe (Semi Final da Amerika.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG