Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


James Rodriguez
James Rodriguez

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City na zawarcin mai tsaron gida na Manchester City, mai suna Joe Hart, wanda a yanzu haka yake Kungiyar kwallon kafa ta Torino a matsayin aro.

Kungiyar Arsenal na neman dan wasan Real Madrid, mai suna Isco, domin yay a taka mata leda a tsakiyar kakar wasan bana da zaran an bude hada hadar sayen ‘yan wasan kwallon kafa a watan Janairu na 2017.

Ita kuwa Chelsea ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £75 domin sayen James Rodriguez daga kungiyar Real Madrid.

Manchester United ta saka Fam miliyan £38 wa dan wasan baya na Benfica mai suna Lindelof.

Itama Manchester City na shirin sayen dan wasan tsakiya na Arsenal Chamberlain inda ta saka kudi har fam miliyan £25, domin sayen dan wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:50 0:00

XS
SM
MD
LG