Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ta Kaya A Wasannin La-liga 2016/2017 Mako Na 16


Ranar jumma'a goma sha shida ga watan Disamba na shekara 2016, an buga wasa a bangaren La-liga na kasar Spain na 2016/2017, 16, Kungiyar kwallon kafa ta Alaves ta doke Real Betis daci 1-0.

A ranar Asabar kuwa Sporting Gijon, ta sha kashi a hannun Villarreal, ne da kwallaye 3-1.
Atletico Madrid ta doke Las Palmas da ci 1-0
Granada 0-2 Real Sociedad
Sevilla ta lallasa Malaga da ci 4-1

Ranar lahadi 18/12/2016 kuwa
Leganes tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Eibar
Deportivo ta samu nasara akan Osasuna da kwallo 2-0
Barcelona kuma ta doke Esponyol da kwallaye 4-1.

A yau kuma za'a kece raini tsakanin Athletic Club da Celta Vigo
Za'a buga wasanne da misalin karfe Tara Saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ke rike da teburin na La-liga da maki 37 a wasanni 15 da tayi.
Sevilla na mataki na biyu da maki 33
Barcelona na mataki na uku da maki 31

A Kasan teburin kuwa Sporting Gijon, na mataki na Goma Sha takwas da maki 12,
Granada na mataki na Sha tara da maki 9
Osasuna na mataki na ashirin da maki 7.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG