Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Cin Kofin Zakarun Turai (UCL) 2016/2017


A wasannin da aka buga jiya 22/11/2016 na cin kofin zakarun turai Kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow ta yi kunnen doki 1-1 da Leverkusesn

Monaco ta samu nasaran doke Tottenham daci 2-1

Sporting Lisbon ta sha kashi a hannun Real Madrid da kwallaye 2-1

Koebenhavn ta yi canjaras 0-0 da Porto

Dinamo Zagreb 0-1 Lyon

Sevilla na da 1 Juventus na da 3

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta lallasa Legia Warsaw da kwallaye 8-4

Leicester City ta doke Club Brugge daci 2-1.

A yau kuma za'a fafata ne tsakanin kungiyoyi guda goma sha shida a gasar (UCL) 2016/2017, Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata karbi bakuncin PSG

Ludo Razgd da Basel, Besiktas kuwa zata kara da Benfica

Napoli zata gwabza ne da Dynamon kyiv

Sauran wasannin kuwa kungiyar kwallon kafa ta Borussia Manglabach za ta kara da Manchester City

Celtic kuma da Barcelona

Atletico Madrid da PSV

Sai Rostov ta gwabza da Bayern Munich

Za'a buga wasanninne da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon najeriya nijar kamaru dakuma kasar Chadi

Wasan da za'a kara tsakanin Besiktas da Benfica da kuma Rostov da Bayern Munich, za'ayi shine da karfe bakwai saura kwata na dare agogon najeriya nijar kamaru dakuma kasar Chadi.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG