Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Falcons Ta Lallasa Mali Da Ci 6 - 0


Kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons, ta Najeriya, ta nakadawa kungiyar kwallon kafa ta kasar Mali, kashi da ci shida da babu a wasan cin kofin kwallon kafar mata na nahiyar Afirka.

Kungiyar Super Falcons, dai a yanzu haka ita ke rike da kambin na wasan kwallon kafa na mata na nahiyar Afirka.

Asisat Oshoala, mai buga kungiyar kwallon kafar mata na Arsenal, ita kadai ta jefa kwallaye hudu inda Francesca Ordega, da Uchechi Sunday, kowace ta jefa kwallo daya.

‘Yan Super Falcons, a wasan su na gaba zasu kara da kasar Ghana, a filin wasa na Limbe dake kasar Kamaru, a ci gaba da kasar na cin kofin nahiyar Afirka na mata.

XS
SM
MD
LG